IQNA

Za A Gudanar Da Taron Watan Azumin Ramadan A Birnin Dubai

22:15 - June 07, 2015
Lambar Labari: 3311885
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da ake fara azumin watan Ramadan mai alfarma za a gudanar da wani shiri da ya kebanci watan a birnin Dubai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na KTimes cewa, a ranar farkota da ake fara azumin watan Ramadan mai alfarma za a kuma a ranar ne ake fara gudanar da wani shiri da ya kebanci watan a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa.

Shi dai wanann shiri ya kunshi abubuwa da dama, da ake gudanarwa domin baki yan kasashen ketare da suke zuwa kasar domin su san wani abu dangane da addinin mulsunci da kuma al’adunsa, da hakan ya hada baje kayyaki na musamman da suka shafi a hakan a cikin kasuwanni da ake budewa da dare.

Laila Muhamad suhail, na daga cikin wadanda suka shirya hakan, ta bayyana cewa, daga cikin abubuwan da ake gudanar a wanann shiri kuwa har da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta musamman da ta kebanci watan Ramadan mai alfarma, da kuma wasu tarkan na musamman da ake shiryawa domin wayar da kan mahalarta.

Wannan shiri dai babbar dama gay an kasashen ketare da suke zuwa birnin a cikin watan Ramadan su san wani abu dangane da addinin muslunci da kuma wasu daga cikin al’adun musulmi.

3311751

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha