Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa, Pop Francis jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika na duniya a ziyarasa a kasar Bosnia da Hozgovina ya yi kira zuwa ga sulhu da zaman lafiya tsakanin dukkanin mabiya addinai, yana mai cewa yana alhini matuka dangane da kisan mutanen kasar a cikin 1992 zuwa 1995.
Ya ce idan al’ummomin duniya suka hadu za su iya zama tare da fahimtar juna, duk kuwa da irin banbancin da ke tsakaninsu, wanda kuma hakan shi ne babbar manufar rayuwa, ka zauna da kowa lafiya, ka baiwa kowa hakinsa, kada ka cutar da wani ko zaluntarsa ko tauye hakkinsa, a lokaci guda kuma kana abin da ka fahimta na akidarka wanda hakan kai ne kawai ya shafa.
Pop Francis ya tafi Bonia ajiya, kuma babbar manufar ziyarar ita ce ganawa da iyalan wadanda suka rasa raykansu a yakin da aka yi a yankin Balkan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dubu 100 a yankin, sakamakon wadannan tashe-tashen hankula.
3311748