Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Abdulalhi Shu’aib babban dakraktan wata kungiya mai gudanar da ayyukan tatatra zakka a Najeriya yana cewa a cikin watan Ramadan za su bayar da buda baki ga mutane kimanin dubu 35 a fadin kasar.
Ya ci gaba da cewa wanann aikin sun saba gudanar da shia kowace shekara, kuma a wanann shekarar ma da yardarm za su yi iyakacin kokarinsu domin taimakawa daga irin kudaden zakka da suke karba daga masu ahnnu da shuni domin gudanar da irin wadannan ayyuka na alkhairi.
Wnanns hiri dai zai fi mayar ad hankali ne a wannan karo wajen taimaka ma mutanen ad suke cikin matasala, musamamn ma wadanda suka baro yakunansu saboda dalilai na tsaro wadanda suka addabi akasar sakamakon bullar yan ta’adda.
A lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma masu kudi a Najeiya sukan taimaka matuka ga wadanda ba su da galihu, ta hanyar ba su kayan abinci da sauran abubuwan bukatar rayuka na abinci da saurana cikin wannan wata da ake azumi, wanda kuma hakan yana taimakawa matuka.
Yanu haka dai akwai mutane kimanin miliyan 3 da suka bar yankunansu suna gudun hijira a cikin Najeriya, fiye da kashi 60 cikin dari na wadannan mutane sun rasa dukaknin abin hannusu, inda suka zaune suna jira daga bayin Allah.
3312188