Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shabakanews.com cewa, biyo bayan wasu kalaman batunci da wani mutum bawahabiye ya yi na kafirta yan shi’a a wani shirin talabijin a Masar, hakan ya jawo kace na ce tsakaninsa da sauran wadanda aka gayyata a cikin shirin na kai tsaye.
Muhamamd Nasir mutum ne da ya shara a kasar ta Masar wajen cin zarafin mabiya tafarkin shi’a, kuma shi ne shugaban wata cibiyar yaki da azhabar shi’a a kasar ta masar, wadda ke gudanar da ayyukanta a kowane lokaci domin kalubalantar mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.
Nasir ya yi wanann batnci da cin zarafi ne a lokacin da yake zanatawa tare da wani shugaban wata kungiya ta sufaye, inda ya ce baya amsa tambayoyin mutane masu akidar sufanci, kamar yadda kuma baya amsa mutanen da ya kira kafirai wato yan shi, inbda ya ambace da munanan kalmomi da bas u misiltuwa ga musulmi.
Tun kafin wanann lokacin dai wannan mutum ya shara wajen nuna kiyayyarsa da yan shi’a kuma suna samun taimako ne da dauki daga masarautar Saudiyya, wadda ke kokarin haifar da rikici a tasakanin al’ummar musulmi a kowane lokaci.
3312632