IQNA

Sheikhul Azhar: Wasu Kasashen Yamma Na Da Hannu Wajen kafa Daesh

23:49 - June 10, 2015
1
Lambar Labari: 3313151
Bangaren kasa da kasa, babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya zargi wasu kasashen yammacin Turai da na Larabawa da hannu a goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Masar.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin saarwa na yanar gizo na Sal Balad cewa, AhmadTayyib jawabinsa ya bayyana cewar wasu kasashen yamma da ‘yan koransu na kasashen Larabawa ne suka cunawa kasar Masar ‘yan ta’adda kuma da kudaden irin wadannan kasashe kungiyoyin ‘yan ta’adda suke ci gaba da aiwatar da munanan ayyukansu na kashe-kashen rayuka da barnata dunkiyar al’umma.

Sheikhin Azhar ya kara da cewar  lokacin wani jawabi a Florence na Italia cewa, maha’inta da shaidan ya hurewa kunne suke daukan nauyin ayyukan ta’addanci a Masar.

A hare-haren ta’addancin baya bayan nan da aka kai kasar ta Masar sun yi sanadiyyar mutuwan jami’an tsaron kasar da fararen hula kimanin talatin tare da jikkatan wasu da dama a yankin Sina.

A bayan kai hare-haren shugaban kasar Masar ya bada umurnin kafa wata runduna da zata dauki alhakin yaki da ta’addanci a kasar.

Ya ce Daesh sun kashe kiristoci da musulmi tare da mayar da yan gudun hiira a kasar Syria, ya ce kafin kiristoci sun fara kashe muuslmi ne.

3312946

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Wannan haka yake. Allah ya meda sharrinsu akansu.
captcha