Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na News Max cewa, kafin wannan lokaci wannan matar ta yi wani makamancin haka wanda ya a ka kai mata a wurin dsa take bake kolin nuna zanen batunci ga manzon Allah (SAW a jahar Texax.
Kungiyar yan ta’adda ta ce ta dauki alhakin kai harin jiya litinin a Jahar a wani bayani da kungiyar ta ish ta fitar a hanyoyin sanarwar da ta saba aikewa da sakwanni, ta ce Mayakan Daular fanci biyu ne suka kai hari akan baje kolin zanen batunci ga manzon Allah a Garland da ke Texas da ke Amurka.
Bayanin ya ci gaba da cewa mayakan sun kwanta dama ne a yayin da su ke musayar wuta da ‘yan sanda. Wani bangare na sanarwar ya gargadi Amurka da cewa a binda za su gani anan gaba zai fi tsanani.
Jami’an tsaron Amurka dai sun sanar da cewa; wasu mutane biyu ne da su ka fito daga mota su ka kai harin ta hanyar bude wuta akan ‘yan sandan da ke tsaron dakin baje kolin hotunan cin zarafin, inda su ka jikkata dan sanda guda.
Wani jami’an tsaro da ke kuma da ziarga-zarigar ababen hawa ya bude wuta akan maharani biyu inda ya kashe su nan take.
3313030