Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Almanar cewa, Hizbullah ta fitar da bayani da a cikisa ta yi kakkausar suka dangane da kisan gillar da ‘yan Takfiriyyan Nusra suka yi wa fararen hula yan Duruz na Syria a cikin makon nan.
Kungiyar ta Hizbullah ta bayyana abin da ya faru da cewa wannan shi ne hakikanin mutanen da ake kira ‘yan ta’adda wadanda kuma da su ne take yaki a cikin kasar Syria, domin, kuw3a idan suka samu dama za su yi fiye da hakana cikin kasar.
Bayanin ya ce kungiyar tana mika ta’aziyya ga dukaknin italan wadanda suka rasa rayuklansu sakamakon wannan mummunar anonba ta ta’addanci wadda ke nufin mayar da al’ummar musulmi da larabawa baya a cikin tarihinsu da ci gabansu na tsawon dubban shekaru.
A ci gaban bayan, kunayar ta jaddada cewa wadanda suka aikata wannan mummunan aiki da kuma wadanda suke daukar nauyinsu domin aikata hakan duk matsayinsu daya a cikin laifin, domin kuwa da wanda ya aikata laifi wanda ya share hanyar yin hakan dukkaninsu sun tarayya.
Yan ta’addan Nusra Front sun kashe yan kabilar Duruz 40 da suka hada da maza da mata da uma kanan yara ba tar da wani dalili ba, sai kawai domin su masu son zubar da jinin mtane ne a duk inda suka saka kafa, wanda akan ya kara fito da fuskarsu da tadabbanci ga duniya.
Daga cikin yara da aka kashe kuwa wadanda shekarunsu ba su wce 10 zuwa 14 ba, wadanda dukkaninsu an same su an dates musu kawuna.
3313294