IQNA

An Bude Wata Tashar Talabijin Da Radiyo Na Muslmi Mai Suna Marah A Najeriya

23:30 - June 12, 2015
Lambar Labari: 3313377
Bangaren kasa da kasa, an bude wata tasha ta talabijin da radio na musulmi a tarayyar Najeriya mai suna Manarh da nufin kara fadar da musulmi a kasar da ma saran kasashen yammacin Afirka.


Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Leadership cewa, a jiya ne aka bude wannan tasha mai suna Manara a birnin Abuja fadar mulkin kasa domin gudanar da shirye-shiye.

Bala Lawai shugaban kungiyar Izala ya bayyana cewa su ne suka bude wannan tashar talabijin da radiyo domin abin da ya kira wayar da kan jama’ar Najeriya da kuma ilmantar da su bisa koyarwa irin ta addinin muslunci.

Ya kara da cewa ta hanyar wannan tasha matasa maza da mata za su samu ayyukan yi da albashi da za su taimaka kansu da danginsu, kamar yadda kuma y ace aikin fadakarwa na wannan tasha ba zai takaita da musulmi ba, har ma wadanda ba musulmi za su amfana.

Fiye da kasha 50 cikin dari na al’ummar Najeriya dai musulmi ne, yayin kasha 40 cikin suke bin tafarkin addinin kirista .

3313298

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha