IQNA

An Yanke Hukunci Kan Makasa ‘Yan Shi’a A Masar

23:53 - June 14, 2015
Lambar Labari: 3314378
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a kasar Masar ta yanke hkuncin dari a gidan kaso kan wasu mutane 31 da suke da hannu a kisan da aka yi wa Sheih Hassan Shata jagoran yan shi’a a Masar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfatah cewa, wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru 14 a kan mutane 23 wadanda ta tabbatar da laifin kashe mabiya mazahabar shia a kasar a shekara ta 2013. Kotun har’ila yau ta wanke mutane 8 wadanda ake tuhuma da kashewa da kuma kona gidajen yan shia dake birnin na Alkahira a wancan lokacin.
Kafin sojoji su kifar da gwamnatin Mohammad Mursi a cikin watan yulin shekara ta dubu biy da sha uku  wadannan muatne sun kai farmaki kan mabiya mazhabar shia a yankin Jiza na birnin Alkahiri, inda suka kashe da dama daga cikinsu.

 

Daga cikin wadanda suka kashe akwai  shuwagabannin ya shia na kasar Shiekh Hassan Shahata wanda ya dade yana shugabancin kungiyar yake kuma gabatar da jawabai a wurare da dama a kasar.

Wannan abin da ya faru yana daya daga cikin abubuwa masu muni a tarihin kasar Masar, musamman ma ganin cewa a lokacin wadanda suke raya kishin islama ne suke rike da gwamnati a lokacin da abin ya faru.

 

Da dama daga cikin masana harkokin shari’a suna ganin ba yi adalcin da ya dace da wadannan mutane ba, domin kuwa da wasu ne suka aikata irin wannan mummun kisan gilla kan wani daban bay an shi’a ba, to da sun fuskanci hkuncin kisa.

A lokacin mulkin hambarraren shugaban kasar ta Masar Muhammad Mursi dai aka kashe Sheikh Shahata tare da dansa da kuma dan uwansa a lokacin da suke taron addini ta hanya dukarsu har suka yi shahada.

 

3314055

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha