IQNA

Ayatollah Sistani ya sanar Da Juma’a Ranar farko Ta Watan Ramadan

23:48 - June 18, 2015
Lambar Labari: 3315922
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci an kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayyana ranar Juma’a ta gobe a matsayin ranar daya ga watan Ramadan mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyya News cewa, tun a jiya ofishin babban malamin addinin muslunci an kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayyana ranar Juma’a ta gobe a matsayin ranar daya ga watan Ramadan matukar ba a gan shi a jiya ba a kasar.

Babban malamin na Iraki ya bayyana cewa ranar jiya laraba it ace ranar da watan shaban ya cika kwanaki talatin daidai, kuma saboda rashin samun wadanda suka ga wata a kasar, a gobe Juma’a ne za a fara azumin watan Ramadan.

Irin wanann sanarwa ta zo a ofishin jagoran juyin juya halin muslunci, amma bayan sanar da cewaa an ga watan, ofishin ya sanar da cewa yau alhamis ne ranar daya ga watan na Ramadan mai alfarma, wanda kuma akasrin kasashen musulmi sun dauki azumin a wannan rana.

3315814

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha