IQNA

An Bude wata gasa Ta Kasa Da kasa Ta Kyawun Rubutun Muslunci A Dubai

23:58 - June 21, 2015
Lambar Labari: 3316992
Bangaren kasa da kasa, an bude gasa kan kyawun rubutu na muslunci a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa kamar yadda aka sanba yi a kowace shekara a lokacin gasar kur’ani ta kasa da kasa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na GTimes cewa, a yau an bude gasa kan kyawun rubutu na muslunci a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa kamar yadda aka sanba yi a kowace shekara a lokacin gasar kur’ani ta kasa da kasa da ake yi wadda ke samun halartar makaranta daga sassa na duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann na daya daga cikin muhimman lamurra da ake gudanarwa a kasar ta haddiyar daular larabawa a lokacin azumin watan Ramadan mai alfarama, inda akan baje kolin kayayykin abubuwa da suke da alaka da kur’ani mai tsarkia  lokacin gasar, inda masu halartar gasar kan duba tare da amfana da su.

Haka nan kuma akn kawo wasu daga cikin abubwan da ake yi a wasu kasashen na al;adu kamar rbutu kan wasu abubuwa na kawata wrare wadanda suke dauke da ayoyin kur’ani ko kuma wasu abubuwa da suke da alaka da muslunci wanda shi ma yana kayatarwa, musamman ma ga wadanda bas u da masaniya kan addini da suke zuwa wurin.

3316293

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha