Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, mabiya addinin muslunci a garin Charlseton sun gudanar da gangai domin nuna goyon bayan ga mabiya addinin kirista bakaken fata da aka kasha a kasar.
A ranar Laraba da ta gabata da dare ne wani matashi farar fata mai suna Dilen Roff ya kai farmaki kan wata majami’ar mabiya addinin kirista bakaken fata a garin Charlston, inda ya kasha mutane 9 daga cikinsu har lahira.
Wannan dai bas hi ne karon farko da ake kai hari kan bakaken fata a kasar Amurka, amma kuma acikin wadannan lokutan abin ya sake tsananta, inda yake daukar sabon salo da ba a saba gani ba, musamamn ganin yadda aka fara kai hari a majami’oinsu.
Har yanzu babu wani abu takamaimai da mahukuntan kasar Amurka suka yi kan batun kare hakkokin bakaken fata, tun bayan da ta bayyana cewa suna fuskantar zalunci daga jami’an yan sanda, inda ake kasha su babu laifin tsaye balantan na zaune.
Irin wannan ta faru a cikin shekarar da ta gabata da kuma wannan shekara da muke ciki, inda jami’an yan sanda suke kasha bakaken fata a cikin birane a gaban jama’a ba tare da wani laifi ba, kuma kotuna suna sakin wadanda suka aikata kisan matukar dai farar fata ne.
Mabiya addinin musluncia kasar Amurka sun fitar da bayani na yin Allawadai da wannan mummunan aiki na ta’addanci, wanda ke nufin cutar da wasu bangare na al’ummar kasar saboda launin fatarsu, da kuma kasantuwarsu marassa rinjaye a kasar.
3317136