Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-jazeeranet cewa, a cikin wadannan lokutan adadin mutanen da suke shiga addinin muslunci a kasar Spain yana karuwa sosai.
Bayanin ya ci gaba da cewa hakan sakamako ne na kokarin da wasu daga cikin musulmin yankin suke yin a fahimtar da al’ummar kasar hakikanin abin da ake kira muslunci, musamamn a wannan lokaci da ta’addanci ya game duniya da sunan muslunci.
Akasarin mabiya addinin muslunci a cikin kasar dai sun fito daga kasashen larabawa na yammacin afrika da kuam wasu daga cikin kasashen yankin gabas ta tsakiya, kuma suna yin iyakacin kokarinsu wajen bayyana gaskiyar wannan addini.
Hanif Scodiro daya ne daga cikin wadanda suka muslunta ba da jimawa ba, ya bayyana cewa hakika ya ji dadin yadda muslmi suke yi mu’amalama da shi, kuma ya fahimci cewa hakan karantarwa ce irin ta addininsu, saboda hakan abin yay i masa tasiri, ta yadda ya gane cewa addinin musluci shi ne kadai addinin gaskiya.
Wanann lamari yana faruwa a dai dai lokacin da masu kiyayya da addinin muslunci suke ta kara kaimi wajen nuna gabarsu da wannan addini, ta hanyr kafa jam’iyyu da kuma kungiyoyi domin yaki da musulunci.
3317201