IQNA

Gudanar Da Wani Shirin Taimako A Cikin Watan Ramadan A Kasar Sudan

23:30 - June 23, 2015
Lambar Labari: 3317963
Bangaren kasa da kasa, wani gungun matasa a kasar Sudan ya sanar da cewa zai gudanar da wani shiri na bayar da taimako mai taken Shfkat da nufin taimaka ma marassa galihu a kasar a cikin wannan wata na Ramadan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kwamafin dillancin labaran Sudan SUNA cewa, wannan shiri zai mayar da hankali ne ga wasu daga cikin ayyuka na gyran masallatai da kuma tamka ma marassa galihu a sassa na kasar, da hakan ya hada da rarraba abinci da kuma bayar da tufafi ga talakawa a lokacin sallar idin karamar salla.

Ibrahim Adam Ibrahim shi ne ministan kula da harkokin zamantakewa na al’ummar kasar Sudan, ya bayyana gaban taron matasan da suke shirya wannan shiri cewa, hakika kasar Sudan tana bukatr shiri irin wannan idan aka yi la’akari cewa kasar tana da mabukata da dama.

Ya ci gaba da cewa babban abin farin cikin shi ne yadda ya zama matasa ne masu kishin kasa suka bullo da hakan, wanda kuma ko shakka babu zai zama abin koyi ga wasu takwarorinsu a wasu bangarori na kasar a lokuta masu zuwa.

Shukar Bashar shi e shugaban kwamitin matasan da suke gudanar da wannan shiri, ya bayyana cewa za su zagaya dukaknin yankuna da ke cikin jahohin kasar baki daya, domin gdanar da abin da suka sanya  agaba a cikin wannan shiri nasu.

Ya kara da cewa, za su yi gyaran masallatai fiye da 3000 a fadin kasar, ta hanyar tsaftace su da share su da wankewa da kuma kakkabe dukkanin kura da ke cikinsu, kamar yadda kuma za su bayar buhunnan abinci kimanin dubu 800 ga mabukata a sassa daban-daban na kasar a cikin wannan wata mai alfarma.

Kasar Sudan dai tana arewa maso gabacin nahiyarr Afirka ne, kuma babban birninta shi ne Khartum, tana jama’a kimanin miliyan 30, kuma kamar kashi 97% daga cikin su abiya addinin muslunci ne.

3317745

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha