IQNA

Wakilin Iran A gasa Dubai Ta Duniya Ya Tsallake Zuwa Mataki Na Gaba

23:50 - June 24, 2015
Lambar Labari: 3318407
Bangaren kasa da kasa, Muhamamd Hussain Behzadfar wakilin Iran agasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya a karo na 12 a birnin Dubai ya tsallake zuwa mataki na gaba.


Ahmad Khosrou masani kan harkokin kur’ani daga ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasa ya bayyana a zantawarsa da kafmanin dillancin labaran iqna cewa, a otel din da alkalan gasar kur’ani ta kasa da kasa ta Dubai suka safka, sun yi wa Muhamamd Hussain Behzadfar wakilin Iran agasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya wasu tambayoyi, kuma duk ya amsa tambayoyin ba tare da wata matasala ba, wannan ya sanya ya tsallake zuwa mataki na gaba a cikin gasar.

Ya ci gaba da cewa alakalan sun yi matashin tambayoyin ne domin su gane matsayinsa da kuma matakin da ya kai, daga irin amsoshin da y aba su, a nan take aa amince da cewa zai shiga gasar a bangare na biyu, domin kuwa ya wuce bangare na farko ta hanyar amsa tambayoyin da ya yi.

Wannan gasa ta birnin Dubai a yau ne za a fara gudanar da ita a hukumace, tare da halartar makaranta da mahardata 80 daga kasashen duniya daban-daban da suka hada da na musulmi da kuma wasu da ban a musulmi ba, inda za su fara karawa da juna.

Muhamamd Hussain Behzadfar shi ne wakilin Iran a gasar, kuma ya kasance daya daga cikin wadanda ake sa ran za su taka rawa matuka domin kaiwa ga mataki na karshe, wanda zai bayar da dama lashe gasar ko kuma zuwa daya daga cikin matakan da ake bukata.

3318287

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha