IQNA

Yan Ta’addan Daesh Sun Kutsa Haramin Makka

23:52 - June 24, 2015
Lambar Labari: 3318409
Bangaren kasa da kasa, wasu masu amfani da hanyar sadarwa ta yanar gizo sun rika yada wani faifan bidiyo da ke yada akidun ta’addan na kungiyar Daesha cikin haramin Makka mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yemen Press cewa, a cikin kwanakin an wasu masu amfani da hanyar sadarwa ta yanar gizo sun rika yada wani faifan bidiyo da ke yada akidun ta’addan na kungiyar Daesh a cikin haramin Makka a lokacin da mutane suke iabda.

Byanin ya ci gaba da cewa mutumin da ya rika yada wannan faifan bidiyon ya rika yin Magana yana kiran mutane zuwa ga abin da suke kira daular muslunci, wadda aka fi sani da kungiyar ta’addancin Daesh, ta hanayar kwadaitar da su tare da yabin Abubakar Baghdadi.

Haka nan kuma ya rika nuna bakar tutarsu wadda ake gane su ta hanayarta, inda yake bayyana kansa a kansa a matsayin daya daga cikin yayan kungiyar da suke yin biyayya ga shugabanta sau da kafa, kuma babu wani abin da mahukuntan kasar suka yi domin bin kadun lamarin.

Da dama daga cikin al’ummomin kasashen duniya musamman ma musulmi, suna da masaniya kan yadda gwamnatin Saudiyya take taka rawa wajen yada munann akidu irin na wanann kungiya da ke kafirta musulmi.

3318343

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha