Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, wanann makamaranta an bude ta ne bayan da mata masu gudun hijira yan Syria suka bukaci hakan.
Makarantar Atfalu shuhada ce ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri na koyar da matan a wani bangare na usamman da aka bude musu bayan da suka kwashe tsawon shekaru suna jiran tsammani danagne da rikiin da aka haddasa akasarsu.
Amina Kusa ita babbar jami’a da ke kula da harkokin ilimi na matan da aka tilasta yin gudun hijira a kasar Syria zuwa cikin kasar ta Turkiya, kuma ta bayyana cewa su ne suka kirkiro shirin kuma za su aiwatar da shi kamar yadda aka shirya.
Kasar Turkiya dai tana da hannu dumu-dumu a cikin hadadsa rikicin kasar Syria, do,in cimma wasu manufofi na ta na siyasa, wanda hakan ya hada da tilasta mutanen da suke kan iyaka da iya yin gudun hijiera zuwa cikin kasarta ta hanyar tura musu yan ta’adda.
Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa gwamnatin kasar it ace kan gaba wajen shiga da ‘yan ta’adda daga kasashen duniya zuwa cikin kasar, wanda kuma abin da suke yi ne yake tilasta fararen hula tserewa, yayin da ita kuma gwamnatin Turkiya take yin talla da hakan domin sukar gwamnatin Syria.
3318303