Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC-Oci.org cewa, Iyad Amin madani babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa, kungiyar ta yi Allawadai da akkakusar murya dangane da kashe Hisham Barakat babban mai shigar da kara na kasar ta Masar ada aka yi a jiya.
Babban mai shigar da kara na kasar Masar ya mutu bayan harin ta’addancin da aka kai wa ayarin motocinsa da safe. Majiyar gwamnatin Kasar Masar ta sanar da cewa; Hashim Barakat ya mutu sanadiyyar raunukan da ya samu daga tashin wani bom akan hanyar ayarin motocinsa dazu da safe.
Tun da fari dai mahukuntan kasar ta Masar sun sanar da cewa Hashim Barakata tare da wasu mutane biyu da su ke yi masa rakiya sun jikkata, kafin daga baya a sanar da mutuwar ta shi.
A wani labarin daga kasar Masar, kungiyar is reshen SIna na kasar Masar ta fitar da wani faifen bidiyo da a cikin ta dauki alhakin kashe wasu alkalai uku a yankin aish.
Faifen bidyon dai ya nuna yadda aka maharani su ka bude wuta ne akan alkalan su uku a cikin a tsakiyar wata Mayu. A cikin wata daya kadai ana kai wa alkalai shida hari a sassa daban-daban na kasar ta Masar.
Muhammad Mumini ya bayayna cewa wanann shi ne hari mafi muni da yan ta’adda suk a kai kasar kan wani babban jami’I a cikin yan lokutan wanda kuma hakan ke nuni da cewa akwai bukatar kwararan matakan tsaro a kasar.
3321471