IQNA

An Fitar Limamai kimanin 40 Masu Tsatsauran Ra’ayi Daga Faransa

23:46 - June 30, 2015
Lambar Labari: 3321654
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Faransa sun a cikin kimanin shekaru da suka gabata an fitar da limamai na masallatai 40 saboda tsatsauran ra’ayinsu


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Star cewa, Bernard Kaznov ministan harkokincikin kasar Faransa ya bayyana cewa cikin kimanin shekaru da suka gabata an fitar da limamai na masallatai 40 saboda tsatsauran ra’ayinsu da suka tunzura wasu domin shiga ayyukan ta’addanci.

Ya ci gaba da cewa za su ci gaba da daukar irin wadannan matakai sakamakon abin da ya farua  garin Lion a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka kai harin ta’addanci a cikin birnin, sakamakon yaduwar masu akidar ta’addanci a kasar.

Wanann mataki da mahukuntan Faransa suke dauka ya kebanci wasu daga cikin limaman masalata ne na masu akidar nan ta kafirta musulmi, wadanda aka fi saninsu da mummunar akidar kafirta musulmi da dukkanin mutane.

Hakan en babban abin da ke sanya su daukar matakin yin kisda kan kowa saboda sun dauki kowa kafiri su kadai ne musulmi da kuma wanda ake da akidarsu ta kafirta musulmi baki daya.

Da dama daga cikin musulmin kasar ta Faransa dai suna nisanta kansu da irin wadannan mutane da kuma ayyukansu amsu muni, idan sukan nuna goyon bayansu ga dukan abin zai kawo zaman lafiya da fahimtar juna a kasar.

3321098

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha