Kamfanin dilalndcin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na Afirka cewa, Muhammad Isa minista mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Algeriya ya bayyana cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin korar limamai daga masallatai masu yada tsatsauran ra’ayin addini a kasar.
Ministan ya ci gaba da cewa yanzu haka an kafa wani kwamiti wanda zai sanya ido a kan dukkanin harkokin masallatai a kasar da jin irin abubuwan da malamai suke fada, da kuma irin lamurran da ake gudanarwa a cikin masallata.
Ya ce yanzu haka an bayar da sunayen wasu limamai guda 55 da suke yada akidar nan ta kafirta musulmi a kasar a cikin masallatansu, wanda hakan yasa ala tilas a dakatar da su kuma a hana gudanar da duk wasu lamurra a cikin masallatai.
Wannan mataki dai ya zop sakamakon irin lamurran da suke faruwa na ta’addanci a cikin kasashen larabawa musamman ma a kasashe da suke makftaka da kasar, inda ake kai hare-haren ta’addan sakamakon yaduwar akidar kafirta muuslmi.
3321755