IQNA

23:08 - July 02, 2015
Lambar Labari: 3322411
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin shi’a na kasar Tanzani za su gudanar da wani jerin gwano domin cikakken goyon bayansu ga al’ummar palastinu da ke fuskantar kisan kiyashi daga yahudawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ippmedia cewa, Hamid Jalalah shugaban kungiyar maiyar tafarkin iyalan gidan manzo a Tanzania ya bayyana cewa, za su gudanar da wani jerin gwano domin cikakken goyon bayansu ga al’ummar palastinu da ke fuskantar kisan kiyashi daga yan mamaya.

Ya ci gaba da cewa yana kira ga dukaknin musulmin kasar Tanzania da su bayar da goyon baya ga al’ummar palastinu da ake kashewa da cin zarafinsu da kuntata musu babu gaira babu sabat, a cikin kasarsu ta haihuwa, y ace yana kira gare s da su yi Allawadai da hakan.

Dangane da halin da halin da al’ummar palastinu suke na nuna musu wariya y ace, ko shakka babu za su gudanar da jerin gwano domin la’antar yahudawan sahyuniya da ke takura musu, domin kuwa babu wata doka ta duniya da bayar da lasisin takura ma wani haka nan.

Daga karshe ya aike da sako zuwa ga shugaban kiristoci Pop Francis da ya dauki mataki na shiga tsakanin yahudawa da kuma palastinawa musamman ma ganin cewa  acikinsuakwai kiristoci da suke fuskantar wariya daga Isra’ila.

3322162

Abubuwan Da Ya Shafa: Tanzania
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: