Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya naaklto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum sabe cewa, a jiya babban Sheikhul Azahar ya bayyana cewa ko alama bai amince da kafirta mabiya tafarkin shi’a ba tare da kiransu da wasu sunaye kamar rafidawa saboda suna son iyalan gidan manzo (AS) kamar yadda wahabiya da masu akidar salafiyanci suke yi.
Ahmad Tayyib ya jadda cewa ko alama bai amince da abin da wasu ke yi ga masu son iyalan gidan amnzo ba(AS) da suke kiransu da sunan rafidawa.
Ya lara da cewa cibiya Azhar cibiya ce tadsdadi da ta hada dukkanin bangarori na musulmi, kuma ba za ta taba zama wurin cin zarafin wani bangare na musulmi ba da kuma haifar da fitinia a tsakanin al’umma.
Dangane da matsalolin da ak ahaifar tsakanin musulmi a tsawon tarihi a tasakanin sunna da shia’ y ace wajibi ne kowane musulmi ya san abin da ya faru a tarihi ta yadda har aka samu wannan bangarori biyu, dukakninsu musulmi.
A kan ya ce dole ne musulmi su zama cikin fadaka, bai kamata a yi ta rikici tsakanin musulmi saboda wasu abubuwa wadanda bas u ne asalin addini ba, bil hasali ma sun faru saboda abubuwa na soyasa har ta kai ga musulmi sun shiga rikici a tsakaninsu.
Ya ce dole ne a kawao karshen kafirta mabiya mazhabar shi’a da wani bangare na muslmi suke yi, domin kuwa a cewarsa hakan bai halarta a shar’ance, kuma yin hakan babban laifi domin kuwa yan shi’a musulmi ne kamar kowane musulmi.
3322878