Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alhaq Net cewa, babbar majalisar malamai a kasar Yemen ta kirayi dukkanin al’ummar zuwa ga halartar babban jerin gwano na ranar Quds aranar yau fadin kasar.
Yau Juma’a milyoyin Al’ummar musulmi za su gudanar da zanga-zangar ranar Qudus a sassa daban daban na duniya. A nan jamhuriyyar musulinci ma’aikatar sadarwar kasar ta bukaci al’ummar kasar da su fito kwonsu da kwalkwatarsu domin nuna cikekken goyon bayansu ga al’ummar Falastinu da kuma raya wannan rana ta Qudus.
Ma’aikatar ta ce a shekarun baya-bayan nan, manyan kasashen duniya masu girman kai sun kirkiro kungiyoyin ta’addanci da dama a kasashen musulmi da kuma kokorin sanya sabani tsakanin suna da shia ba don komai ba sai don bata sunan musulinci da kuma sanya sabani tsakanin musulmi, don haka, wajibi musulmin duniya su farka .
Ana gudanr da wannan ranar ta Qudus a kowace juma’a karshe ta watan Ramalana, saidai a wanna karo za’a gudanar da ita yau juma’a saboda mai yiwa jum’a mai zuwa ta kasance karamar salla.
3326173