IQNA

Cibiyar Musulmin Colney A London ta Kirayi Jama’a Zuwa Buda Baki

23:49 - July 11, 2015
Lambar Labari: 3326795
Bangaren kasa da kasa, cibiyar mabiya addinin muslunci a yankin Colney na birnin London da suka hada musulmi da kuma wadanda ba mabiya addinin musulunci ba zuwa buda baki.


Kamfanin dillancin labaran iqna yahabarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Herts Advertiser cewa, wannan buda baki za a gudanar shi gobe idan allah ya kai mu a ginin bababr cibiyar  (The London Colney Islamic Centre)  da ke cikin birnin London ya kunshi mutanen birnin da suka hada musulmi da kuma wadanda ba mabiya addinin musulunci ba.

Wanann cibiya dai tana (Sopwell Community Trust) ne da take daukar nauyin gudanar da irin wadannan ayuka da nufin kara wayar da kan mutane kan addinin muslunci, musamman a wannan lokaci da ake samun rashin fahimta kan wannan addini.

Baya ga wannan buda kuma, a ranar Juma’a mai zuwa da ake sa ran a ranar za  agudanar da sallar idin na karamar salla ta wannan shekara, wannan cibiya za ta shirya wani zaman makamncin wannan, tare da gayyatar mutanen yankin da suka musulmi da wadanda ba musulmi domin cina bin cin salla kara.

Wanann lamari yana bababn tasiri ga wadanda suke halatar wurin, musamamn dai wadanda ba musulmi ba domin hakan yana sanya su gane banbancin da ke akwai tsakanin addinin muslunci da kuma tunaninsu a kansa da kuma yadda suke kallon musulmi.

3326587

Abubuwan Da Ya Shafa: london
captcha