Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, kwamitin tsare-tsare na majalisar haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da gida gidaje 192 da kuma otel mai dakuna 480 a cikin wata makabratr musulmi mai tsohon tarihi a yammacin birnin Quds mai alfarma.
Bayanin y ace gwamnatin yahudawan ta dauki wannan mataki da nufin yin wata sabuwar tsokana ga musulmi, domin kuwa daukar wannan mataki ba abu ne da mabiya addinin muslunci za su amince da shi ba, musamman ma ganin cewa wannan makabarta na da tsohon tarihi ga musulmin yankin.
Haramtacciyar kasar Isra’ila tana yin amfani da irin goyon bayan da take samu daga manyan kasashen duniya wajen cutar al’ummar palastinu tare da danne hakkokinsu a dukkanin bangarori, ba tare da an iya gurfanar da ita a gaban shari’ar domin kwatar musu hakkokinsu ba.
Babbar cibiyar kare hakkokin palastinawa ta sanar da cewa, za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin kalubalantar wannan mataki na zalunci, kamar yadda ta jaddad cewa daga cikin hanyoyin da za ta bi kuwa har da na shari’a a mataki na farko.
Cibiyar ta ce a tarihin yankin baki babbu wani wanda ke ja ko musun cewa wannan makabarta ba ta mabiya addinin muslunci ba ce, kamar yadda kuma dukkanin larabawa suna da hakkin a cikinta.
3327934