IQNA

Bankin Muslunci Ya Fadada Ayyukansa A Cikin Kasar Tanzania

23:56 - July 14, 2015
Lambar Labari: 3328210
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da ayyukan da yake gudanarwa NBC wato bangaren harkokin kasuwanci na bankin muslunci a kan abubuwa kimanin 10 a Tanzania ya kara bunksa ayyukansa a tsibirin Zanjbar.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gio na Allafrica cewa, Nasir Mas’ud babban daraktan NBC bangaren kula da harkokin kasuwanci na babban bankin muslunci ya bayyana cewa suna kara bunkasa harkokinsu a cikin kasar ta Tanzania.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wasu yan kasuwa da kuma masu saka hannayen jari na kasar, ya bayyana cewa ko shakka babu babbana bin da ke a gabansu a halin yanzu shi ne tabbatar da cewa ayyukansu sun kara fada a cikin wannan kasa.

Nasir Mas’ud y ace yanzu haka sun samu damar girka bangarori na ayyuka musamman ba a bangaren harkokin noma, wanda mutane suke mayar da hankalia  akansa matuka  acikin kasar, kuma mabiya addinin muslucni sun fi mayar da hankali kansa.

A kan haka y ace suna kokarin ganin an samu wani shiri wanda zai kebanci wannan bankia  banagaren aikin noma tare da hadin gwiwa da mahukunta da kuma manoma masu zaman kansu, ta yadda kowane bangare zai amfana.

Kasar Tanzania dai kimanin kasha 60% cikin na mutanen kasar dai mabiya addinin muslunci ne.

3327664

Abubuwan Da Ya Shafa: tanzania
captcha