Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran palastinu cewa, babban kwamitin da ke kula lamurran addini da kuma fatawa na palastinu ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya ke cewa yahudawan sahyniya suna bababr barazana ga wanzuwar masallacin quds ta hanyar hankoron rusa shi.
Dagane da wannan batu hakan nan kuma rahoton ya ce gwamnatin yahudawan ta dauki wannan mataki da nufin yin wata sabuwar tsokana ga musulmi, domin kuwa daukar wannan mataki ba abu ne da mabiya addinin muslunci za su amince da shi ba, musamman ma ganin cewa wannan masallaci na al’ummar musulmi ne baki daya.
Hukumar yahudawan tana yin amfani da irin goyon bayan da take samu daga manyan kasashen duniya wajen cutar al’ummar palastinu tare da danne hakkokinsu a dukkanin bangarori, ba tare da an iya gurfanar da ita a gaban shari’ar domin kwatar musu hakkokinsu ba.
Babban malamin da ke kula wannan babbar cibiyar fatawa da ma kare hakkokin palastinawa ya sanar da cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar wannan mataki na zalunci da danniya da yahdawan suke nunawa.
Haka nan kuma sun yadda cewa daga akwai hanyoyin da za su bi da kuma matakin da za su dauka kuwa wajen tunkarar wannan lamari mai matukar hadari da barazana ga kaddarorin al’ummar muslmi.
3332417