Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah news cewa, a jiya ne yan ta’addan daesh suka sare kan Sheikh Nakshabandi daya daga cikin malaman addinin muslunci kuma limamin masallacin Alsalihin da ke yammacin birnin Mausil da ke karkashin ikonsu.
Wani wanda ya bukaci da a sakaya sunansa ya bayyana cewa, yan ta’addan sun kashe wannan malami ne bisa hujjar cewa ba ya bin irin koyarwar da suka yarda da ita, kuma suka bayar da umarni da a yi aiki da ita a yankin, a kan hakan haka hukuncin kisa ya ha kansa.
A ranar Litinin da ta gabata ce yan ta’addan suka harbe daya daga cikin malaman yankin Shekh Najmuddin Kan’an Aljaburi kuma limamin masallacin Alhumaid, ta hanyar yin amfani da harsashen bindiga a kansa.
Yan ta’addan sun kash malamai da dama a Masil tun bayan kwace iko da yankin a cikin watan Yunin shekara ta 2014, tare da taimakon wasu daga cikin kasashen da ke makwabtaka da kasar ta Iraki.
Ya zuwa yanzu dai yan ta’addan sun kashe malamai da kuma al’umar gari masu tarin yawa bisa hujjoji daban-daban, musamman ma dais aba umarininsu da kuma kallonsu a matsayin wadanda ba kan sahihin tafarki suke ba, domin kuwa suna kallon kowa a matsayin kafiri sai dai wanda ya shiga cikinsu.
3332435