IQNA

23:22 - July 26, 2015
Lambar Labari: 3335537
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani taro kan masallacin Quds mai alfarma a birnin Nuwakshut na kasar Mauritaniya a jiya tare da halartar masana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, manufar gudanar da taron ita ce kara tabbatar da alaka da ke tsakanin al’ummomin kasar da kuma yan uwansu palastinawa da ke karkashin danniya.

 

Muhammad Gholam Wuld Haj Sheikh shi ne shugaban cibiyar kula da harkokin quds ta kasar Mauritaniya da ke zaman kanta, wanda kuma ita ce ta shirya wannan taro da ke samun halartar masana daga sassa na kasar domin gabatar da jabawai da makalolinsu a wannan taro.

A lokacin da yake gabatar da nasaa a jawabin a gaban taron, shugaban cibiyar ya bayayan cewa suna bin dukkanin hanyoyin da suka kamata domin tabbatar da cewa sun raya tannin quds a cikin zukatan al’umma, na kasarsu ne ko kuwa na sauran kasashen musulmi ne da na larabawa, ta hanyoyin shirya irin wadannan tarka, da kuma rbuta makaloli da ake wallafawa.

 

Shi dai wannan taro na nufin isar da sakon al’ummal palasdinu ne da ke karkashin zalunci da danniya ta yahudawan sahyuniya da suke kokarin mayar da kasar musulmi mallakinsu, tare da keta  alfarmar wrare masu tsarki mallakin msulmi  akowace rana, sakamakon goyon bayan da ske samu daga manyan kasashe da kuma wasu daga cikin gwamnatocin kasashen larabawa.

Tuna  cikin shekara ta 2009 wannan cibiya ta yi ta fada tashin ganin a yanke duk wata alaka tsakanin kasarsu da kuma harmtacciyar kasar Isra’ila, tare da kare dukkanin hakkokin palastinawa da aka taye musu.

 

A cikin shekara ta 1999 ne dai aka kafa wannan kungiya, da nufin samun hadin baki tsakanin al’ummar kasar da zai kai ga samo yancin palastinawa a matsayi na kasa da kasa.
3335123

Abubuwan Da Ya Shafa: Mauritania
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: