Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OnIslam cewa, an gudanar da wannan taro ne a birnin Abuja fadar mlkin kasar mulkin kasar tare da halartar jama’a da dama.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da malaman addini da kuma wasu masana na ciki da kuma wasu daga kasashen ketare, inda aka gabatar da jawabai wanda shi kansa jagoran tafiyar Sheikh Ibrahim Zakzaki ya gabatar da nasa jawabin domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu.
A cikin shekarar da ta gabata ce dai alokacin gudanar da jerin gwano a ranar quds ta duniya a birnin Zaria da ke cikin jahar Kaduna, aka kai harin kan masu wannan jerin gwano, inda mutane 35 daga cikinsu ka yi shahada, daga cikinsu kuwa har da 3 wadanda ‘ya’yan sheikh Ibrahim Zakzaki ne.
Mabiya mazhabar shi’a a Najeriya sun bukaci da a gudanar da bicike na adalci kan wannan lamari, domin gano wadanda suke da hannu cikin lamarin domin hukunta su, bisa laifin da suka aikata, lamarin da ya sa suke yin Allawadai da shiru da mahukunta suka yi kan lamarin.
A nasu bangaren jami’an gwamnatin najeriya sun ce suna gudanar da sahihin bincike dangane da abin da ya faru, duk kwa da cewa shekara daya ta wuce da faruwar lamarin, amma dai har yanzu babu wani sakamako na wannan bincike daga mahukuntan.
3335657