IQNA

‘Yan Sunna A Iraki Sun Shiga Cikin Sojojin Sa Kai Na yaki Da Daesh

23:56 - July 29, 2015
Lambar Labari: 3336908
Bangaren kasa da kasa, kimanin yan sunna 6000 ne suka shiga cikin sojojin sa kai na kasar Iraki somin yaki da yan ta’addan Takfiriyyah Dashe suka fitini yankunansu.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar PressTV cewa, Habib Al-Tufri wakilin majalisar tsaron kasa ya ce sojojin kasar Iraki tare da taimakon dakarun sa kai suna ci gaba da fatattakar 'yan ta'addan Daesh Daesh a cikin yankuna da daman a lardunan Salahuddin da kuma Anbar da ke arewacin kasar.

Habib Al-tufri a zantawarsa da wasu kafofin yada labarai a yammacin jiya, amiri kwamnadar rundunar sa kai ta adar ya bayyana cewa, an samu gagarumin ci gaba a cikin makonni biyu zuwa uku da suka gabata, inda rundunar sojin Iraki tare da taimakon sojojin sa kai daga dukkanin bangarori na al'ummomin Iraki suke ci gaba fatattakar 'yan ta'addan Daesh.

A bangare guda kuma ya kore abin da ya kira farfagandar da wasu kafofin yada labarai suke yadawa, a kan cewa abin da ke faruwa a Iraki yaki ne tsakanin yan sunna da 'yan shi'a, inda ya ce dukkanin sojojin sa kai da suke taimaka ma rundunar sojin Iraki  da suka fito daga lardunan Salahudin da Anbar 'yan sunnah ne, domina cewarsa dan ta'adda bai bance dan sunna ko dan shi'a ko bakurde ko kirista, aikinsu shi ne kisan dan adam ba tare da rahma ba.

A jiya ma kimanin mutane 20 daga yan ta’adda aka hallaki ayankin Aljawi da ke cikin Tikrit a gundumar salhuddin.

3336653

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha