IQNA

An Gudanar Da Wani Zama A Yankin Qatif Na Mabiya Mazhabar Shi’a A Saudiyya

23:12 - July 30, 2015
Lambar Labari: 3337037
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zama na bin kadun ayyukan kur’ani mai tsarki a yankin Qatif da ke gabacin kasar Saudiyya na mabiya mazhabar iyalan gidan manzo.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman ne a Husainiyar Babul Hawa’ij da ke yankin Qatif a gundumar Shakuri kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.

Mutane daga yankunan Ummu Hammam, Aujam, Dammam da kuma Qatif duk sun samu halartar wannan zaman taro na ayyukan kur’ani mai tsarki.

Daga muhimman abubuwan da taron ya mayar da hankali a kansu akwai batun yadda za a raya tare da farfado da ilmin Tajwidin karatun kur’ani bisa ka’idojinsa da kuma kawar da yadda wasu suke kyamar hakan.

An karfafa gwaiwar mutane kan muhimmancin karatun kur’ani mai tsarki tare da koyon kaidojin karatun, da kuma sanar da wani shiri wanda zai taimaka ma mutane wajen ci gaba da binsa.

A karshen taron Ali Hashem wanda shi ne babban daraktan cibiyar da ta dauki nauyin shirya wannan taro, ya bayyana cewa haki an sau samu nasarar da ake bukata wajen fara aiwatar da wanann shiri, kuma da yardarm Allah hakan zai ci gaba.

3336819

Abubuwan Da Ya Shafa: qatif
captcha