IQNA

20:15 - August 01, 2015
Lambar Labari: 3337641
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da kisan gillar da yahudawan sahyuniya suka yi wa wani jariri ta hanyar kone shi da wuta a jiya a yammacin kogin Jodan.

Kamfanin dillancin labaranb Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na OIC cewa, a cikin wata sanarwa ta gagagwa da mai Magana da yawun kungiyar ya fitar y ace kungiyar na yin Allawadai da wannan aiki na ta’addanci da yahudawan suke aikatawa kan muuslmin palastine musamman kisan karamin jariri dan shekara daya da rabi da suka yi mai suna Ali Sa’ad Dawabisha dan wansa da shekaru 4 da iyayensa ta hanyar kone shi da wuta.

 

Tare da kiran sauran al’ummomin musulmi da su mike domin taka wa yahudawan sahyuniya birki kan wannan ta’addanci da suke aikatawa.

Yahudawan sun jefa bama-baman kwalba kan gidan mahafan yaron, lamarin da ya yi sanadiyyar konewar gidan, inda mahaifan yaron suka jikkata shi kuma yakone da wuta har ya rasa ransa.

 

Gwamnatoci da daman a duniya da suka hada har da masu goyon bayan ta’addancin yahudawan, sun da bayar  da kariya ido rufe ga irin wadanna yauka da Isra’ila take aikatawa, a yau sun yi tir da Allawadai da hakan, tare da bayyana kone wannan jariri da cewa aiki ne ta’addanci da dabbanci.

Kamar yadda ita ma kungiyar kasashen larabawa ta fitar da bayani da ke yin Allawadai da hakan, tare da yin kira da a dauki matakin ladabtar da Isra’ila kan wannan mummunan aiki.

 

3337238

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: