IQNA

Azhar Ba Ta San Da Zaman Kungiyar Malaman Musulmi Ta Duniya Ba

20:21 - August 01, 2015
Lambar Labari: 3337643
Bangaren kasa da kasa, Abbas Shoman mataimakin babban malamin ciyar Azhar ya bayyana cewa ba su san da zaman kungiyar malaman musulmi ta duniya karkashin Yusuf Qardawi ba.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Fito cewa, Abbas Shoman mataimakin babban malamin ciyar Azhar a lokacin da yake wani jawabi ya bayyana cewa ba su san da zaman kungiyar malaman musulmi ta duniya karkashin Yusuf Qardawi ba kuma suna yin kira da masu shiga wannan kungiya da su yi hattara.

Ya ci gaba da cewa kungiyar da ake kira jabha ta malaman Azhar da kuma kungiyar malaman musulmi ta duniya karkashin Yusuf Qardawi ba su da wani matsayi a idon wannan ciyar ta Azahar, domin kuwa bas u kan kaida, kuma suna gudanar da ayyukan da suka saba wa koyarwar addini.

Dangane da yadda wadannan kungiyoyi suke gudanar da ayyukansu amatsayi na kasa da kasa kywa, ya bayyana cewa su ne kan gaba wajen haifar da matsaloli da dama a cikin kasashen musulmi tare da tunzura mutane zuwa ga ayyukan ta’addanci.

Malamin ya ce wadannan kungiyoyi daidai suke da sauran kungiyoyi na ta’addanci a duniya, domin kuwa aikinsu shi ne kawo rikici da rashin fahimta a tsakanin al’ummar musulmi, tare da jawo kashe jama’a babu gaira babu sabat.

Ya kara da cewa wadanda suka shiga cikin wannan shirme sun san cewa ba su wani matsayi, ko da mutuwa suka yi daga bangaren Azhar a hukumance babu wanda zai halarci janazarsu, saboda abin da suke aikatawa.

3337525

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha