Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabi21.com cewa, Sa’adi Albashir wakilin kugiyoyin musulmi masu kare hakkokin palastinwa ya bayyana cewa suna yin shirin domin shigar da kara kan haramatacciyar kasar Isra’ila a gaban kuliya kan ayyukanta na ta’addanci musamman kone jaririn da aka yi.
Ana ci gaba da mayar da martini a fadin duniya dangane da kisan jariri dan shekara daya da rabi da haihuwa da yahudawan sahyuniya suka a yi a Juma’ar da ta gabata, ta hanyar kone shi da wuta, bayan da suka kona gidan mahaifinsa kurmus.
Yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi ne suka kai harin a garin Doma da ke kudancin birnin Nablus da ke yankin yammacin Kogin Jordan, inda suka kona gidan Sa’ad Dawabisha a lokacin da yake cikin gidan tare da iyalansa, inda suka kona su baki daya, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar kamarin dansa mai suna Ali, yayin da shi kuma da matarsa da babban dansa mai suna Ahmad suka samu munanan raunuka, sakamakon kunar wuta.
Wannan wakilin kungiyoyin musulmin y ace suna da hakkin su shigar da kara kan wannan aikin ta’addanci da aka aikata kan wannan jariri bapalastine da ma sauran ayyukan zaunci da al’ummar palastine ke fuskanta.
3338024