Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na oic-oci.org cewa, a bayanin da kungiyar hadin kasashen musulmi ta sanar ta bayyana cewa a shirye take domin gudanar da babban taron shugabannin kasashen kungiyar domin tatatuna halin ake ciki a birnin Quds.
Bayanin ya ce shugaban palastinawa Mahumud Abbas ne ya bukaci gudanar da wannan taro, domin yana da matukar muhimamnci, domin batun palastinu shi ne farko a wajen a kowane lokaci, kuma za a yi dubi kan halin da ake da yadda yahudawa suke ta kara kaimi wajen cutar da palastibnawa da kuma amamye musu yankuna.
Haka nan kuma kungiyar ta ce dukkanin mahalarta taron za su tattauna batun kawo karshen mamaye yankunan palastinawa da ma saurana yyuka na zalunci da ake yi kan wanna al’umma na tsawon shekaru,, inda za tattauna hanyoyin da za a bi domin yin hakan.
Yanzu haka dai kungiyar ta sanar da shirinta, kuma ta mika batun ayyana lokacin fara taron ga mahukuntan kasar Morocco da ke da masafkin baki, domin sanar da sauran kasashe.
Taron dai za a gudanar da shi ne a matsayin taron gagagwa, kuma ana sa ran zai samu halartar shugabannin kasashen musulmi mambo a wannan kungiya.
3339686