IQNA

Mata Musulmi A Najeriya Ba Su Amince Da Dokar Hana Saka Hijabi Ba

22:05 - August 09, 2015
Lambar Labari: 3340686
Bangaren kasa da kasa, wata kungiyar kare hakkokin mata musulmi a Najeriya tana fafutukar ganin ta kalubalanci matakain hana mata saka hijabin muslunci a kasar saboda batun Boko haram.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na today.ng cewa, Hajiya Amina Amoti shugabar cibiyar kare hakkokin mata musulmi a Najeriya ta ce za su ci gaba da  fafutukar ganin sun kalubalanci matakain hana mata saka hijabin muslunci a kasar saboda batun hakan bas hi da alaka da Boko haram sai dai wani abun na daban.

Ta ce wannan mataki na yunkurin hana mata saka hijabi bai dace ba, kuma dukkanin muuslmi a kasar ba za su yi kasa a gwiwa wajen fuskantarsa ba da dukkanin karfinsu, domin tababtar da cewa ba a danne hakkokinsu ba.

Hare-haren bayan nan da mayakan kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram suka kai a wasu yankuna a rewa maso gabacin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shi ne baban dalilin sanar da daukar wannan mataki.

Tun bayan sanar da matakin a wasu yankunan kasar musulmi suke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu, tare da neman a yi amfani da wasu hanyoyi na tantance yan ta’adda, maimakon takura mata muslmi masu saka hijabin musluncia  kasar da sunan ana yaki da yan ta’adda.

Masu kai hare-haren dai akasari mata ne kuma suna yin amfani da hijabin wajen kai harin a kan jama’ farareen hula da ma sauran wrare na hahadar jama’a a wasu yankunan asar, wanda hakan yake tsorata jama’a  aduk lokacin da aka mace da hijabi ta shigo cikin mutane.

Mabiya addinin muslunci baki daya suna yin tir da Allawadai da ayyukan ta’addanci na kungiyar ta Boko haram, tare da kiran jami’an tsaro da su kara matsa kaimi wajen tunkarar wannan lamari, domin samun zaman lafiya  akasar.

Adadin musulmin Najeriya dai ya kai kasha 55 cikin dari, yayin da kiristoci kuma ya kai 40 a cikin mutane miliyan 140 n dukaknin al’ummar kasar.

3340432

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha