IQNA

Zama Tsakanin OIC Da Kuma ISESCO Kan Batun Fuskantar Ayyukan Ta’addanci

22:09 - August 09, 2015
Lambar Labari: 3340688
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zama tsakanin kungiyar kasashen musulmi da kuma cibiyar buknakasa ilimi da ayyukan al’adun muslunci a kan ayyukan ta’addanci a birnin Jidda na kasar Saudiyya.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nab okra-news.com cewa, a jiya ne aka gudanar da zama tsakanin kungiyar kasashen musulmi da kuma cibiyar bunkasa ilimi da ayyukan al’adu a ofishin kungiyar da ke  birnin Jidda.

Rahoton ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan zama dai ita ce tatatuna abubuwa da ske faruwa yanzu haka a cikin kasashen musulmi, inda ta’addanci yak e ci gaba da yin karfi da yaduwa sakamakon tsatsauran ra’ayin addini da ya yi katutu.

Akasarin kasashen musulmi suna ganin cewa yin amfani da wasu kasashen larabawa ke yi da kudadensu wajen yada akidar kafirta musulmi shi ne babban abin da ya kara yada wannan mummunan akida atsakanin musulmi a duniya.

Wasu daga cikin masana da suke wakiltar wasu cibiyoyi na ilimi da suke bayar da shawarwari a kasashen musulmi da kuma kungiyar hadin kan kasashen musulmi sun bayyana cewa, dole ne a yi yaki da akidar kafirta muslmi kamar yadda ake yin yaki da makami kan ‘yan ta’adda.

Da dama daga cikin musulmi a duniya dai bas u amince da wannan mummunar akida ba wadda ta samo asali daga koyawar wahabiyawa da ke kafirta duk wani musulmi da bai bi irin akidarsu ba, wadda akasrin al’mmomin muuslmi a dniya bas u yarda da it aba.

Mostafa Ahmad Ali shi ne babban jami’i mai kula ayyukan kungiyar hadin kan kasashen musulmi da suka shafi kasashen ketare, ya bayyana cewa zaman ya mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi domin fuskantar wannan barazana ta ta’addancia duniyar musulmi.

3340016

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha