Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, shugaban najeriya a lokacin wani jawabi a Kano ya bukaci da a saka wasu daga cikin littafan addinin muslunci da suke koyar da tarbiya a wajen koyar da yara a makarantun gwamnati.
Ya ci gaba da cewa yin amfani da abin da zai taimaka wajen kara tarbiyar daliban makarantu na daga littafan muslunci da aka rubuta domin tarbiya da koyar da kyawawan dabiu wajibi ne.
Tun bayan da shugaban na Najeriya ya karbni shugabancin kasar a watannin baya, ya mayar da hankali matuka wajen iunganta duk abin da yake ganin zai dace da kasar da kuma al’ummarta, wanda kuma batun ilimi yana daga ciki.
Wannan shiri na shugaba Buhari dai zai shafi makarantun gwamnati ne kawai, duk kuwa da cewa ana gudanar da shiri makamancin hakan a makarantun yankunan arewacin kasar, wadanda akasarinsu mabiya addinin muslunci ne.
Al’ummar Najeriya musamamn ma dai musulmi daga cikinsu sun bayyana gamsuwarsu da wannan shiri na shugaba Buhari na koyar da waus daga cikin littafan addinin muslunci a cikin makarantun gwamnatin kasar.
A nata bangaren babbar cibiyar da ke kula da ayyukan malamai masu koyarwa a makarantu ta yi na’am da wannan shawara ta shugaba Buhari, tare da bayyana cewa a shirye take ta aiwatar da hakan.
Najeriya dai tana da yawan mutane da ya kai miliyan 140 wadanda 55 daga cikinsu mabiya addinin muslunci ne, 40 daga ciki kuma mabiya addinin kirista ne.
3341488