IQNA

An Bude Baje Kolin Fina-Finan Muslunci A Birnin Tehran

22:30 - August 16, 2015
Lambar Labari: 3344937
Bangaren kasa da kasa, an bude wani baje koli na fina-finan muslunci da kayayyakin al’adu a gefen taron cibiyar radiyo da talabijin ta kasashen msulmi a Tehran.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat daga wurin taron cewa, a yau ne aka bude babban taron cibiyar gidajen radiyo da talabijin na kasashen musulmi a birnin Tehran na kasar Iran, tare da halartar jami’an gwamnati gami da masana kan harkokin yada labarai da ala’adu na ciki da wajen kasar.

Taron wanda ake gudanarwa a karo na takwas baya ga jami’ai na cikin gida, taron yana samun halartar baki daga kasashen da dama, mahalarta 90 tare da nuna kayan al’adu da fina-finai daga cikin kasashen musulmi, da suka hada har da kasashen na nahiyoyin asia da sauransu.

Babbar manufar taron dai ita ce tattauna hanyoyin yada labarai na gaskiya ga al’ummomin duniya, tare da fadakar da su muhimman lamurran da suka shafi duniyar musulmi, haka nan kuma taron ya kunshi  bangaren baje koli na kayayyakin al’adu da yada labarai da kuma fina-finan muslunci.

A wannan karon taron dai yana da taken a shekarar bana yana da taken “Manzon Rahma sakon kafofin yada labarai na gwagwarma” kuma yana gudana a dakin taron da hukumar radiyo da talabijin ta jamhuriyar muslunci.

3344713

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha