IQNA

Tabbatattar Akidar Wahabiyawa Ita Ce Kawar Da Mabiya Ahlul Bait (AS)

22:33 - August 16, 2015
Lambar Labari: 3344938
Bangaren kasa da kasa, sabanin da ke tsakanin wahabiyawa da mabiya Ahll bait(AS) bana siyasa ba ne sabani ne mai zaman kansa na kiyayya da gidan amnzon Allah da kuma hankoron ganin mabiya tafarkin iyalan wannan gida mai tsarki.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, Nuri Maliki mataimakin shugaban kasar Iraki a jawabinsa na bude taron cibiyar Ahlul bait (AS) a karo na takwas ya bayyana cewa, babban abin da ke gaban gwamnatin Saudiyyah a halin yanzu shi ne taimakon kungiyoyin ‘yan ta’adda a ko’ina suke cikin fadin duniya.

Ya ce kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi duniya a yau baki daya da suka hada da Taliban, Alkaida, Boko Haram, Alshabab, Daesh, Alnusra da sauransu duk masu dauke ne da akidar wahabiyanci, kuma suna samun taimakon kudade da karfin gwiwa ne kai tsaye daga kasar saudiyya, babu mai musun haka a duniya.

Haka nan kuma ya ce maganar gaskiya ita ce duk wannan sabanin da ke tsakanin wahabiyawa da mabiya Ahll bait(AS) ba wai magana ce ta siyasa ba sabani ne mai zaman kansa na kiyayya da gidan mannzon Allah da kuma hankoron ganin bayan mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.

Ya ci gaba da cewa idan aka yi la’akari da matsyin Saudiyyah a halin dangane da abin da faruwa a cikin kasashen yanking abas ta tsakiya da ake shirin rusawa ta hanyar yin amfani da ‘yan ta’adda, za a ga cewa babu inda babu hannun Saudiyya a ciki dumu-dumu.

Daga ciki kuwa har da kasashen da suke makwaftaka da ita kai tsaye, inda a halin yanzu ita da kanta take amfani da jiragen yaki da makamai masu linzai tana kaddamar da hare-hare kan gidajen jama’a da talakawa domin tabbatar da cewa ta kawar da duk wanda baya bin salon akidarta ta wahabiyanci.

Maliki ya kara da cewa dangane da wadanda suke tunanin za su zauna kan teburin tattanawa tare da haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma suke ganin za su iya rayuwa da ita, to suna tafka baban kure, domin kuwa tana neman hanyar da za ta ga bayansu ne, balanta sun mika kansu gare ta.

3344637

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha