IQNA

Babu Wani Dalili Da Zai Hana Kusanto Da Fahimta Tsakanin Shi’a Da Sunnah

20:08 - August 18, 2015
Lambar Labari: 3345840
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Ahmad Karimah daya daga cikin manyan malaman fikihu na cibiyar Azahar bayyana furucin Sheikhul Azhar da Moqtada Sadr ya bayyana cewa babu abin da zai hana a samu fahitar juna tsakanin shi’a da sunna.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, Sheikh Ahmad Karimah ya bayyana cewa maganganun da Moqtada Sadr ya yi suna da muhimmanci, kuma ya kamata a kara karfafa alaka tsakanin bangarorin musulmi.

A jiya ne shehin malamin wanda daya ne daga cikin manyan malaman fikihu na cibiyar Azahar bayyana furucin malaman biyu da ya gudana kan hadin kai da cewa yana da kyau, kuma babu abin da zai hana a samu fahitar juna tsakanin bangarorin tafarkin biyu.

Ya ci gaba da cewa abin da ya hada bangarorin biyu ya fi abin da y araba su, saboda haka nauyi ne da ya rataya malaman dukkanin bangarorin biyu su mike tsaye su kawo karshen nisantar juna, domin samun hadin kai tsakanin al’ummar musulmi baki daya ta yadda za a zama tsintsiya daya madaurinki daya.

Sheikh Ahmad Karimah ya ce a lokacin da Sheikh Muhammad Shaltut yana raye ya mayar da hankali matuka wajen kiran dukkanin bangarori na sunna da shi’a zuwa ga hada kai, domin yi wa addinin muslunci aiki tare ba tare da wata tsangwama ba.

3345109

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha