Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan News cewa, ‘yan shi’a a kasar Masar na shirin tsayawa takarar zaben majalisar dokokin kasara karkashin inuwar jam’iyyar sufaye wadda ta hada mabiya darikun sufanci na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa mataki na farko na zaben majalisar dokokin kasar Masar zai fara ne a cikin watan Mehr, kuma mabiya tafarkin shi’a zasu tsayar da na ‘yan takarar da suka hada da Muhammad Damrdash daga yankin Asyut, sai kuma Haisam Abdunnabiyi daga Asbatiyya gami da Atef Almagawiri daga Zaqhariq.
Ala’u Saed kakakin ‘yan salafiyya a kasar Masar ya yi kakkausar suka kan hakan, tun kafin wannan lokacin dai mabiya tafarkin shi’a akasar ta Masar sun nuna bukatar tsayawa neman kujeru a majalisar da saun bangarori na siyasa ta hanyar zabe, amma kuma suna fuskantar matsaloli daga mahukunta, wadanda suka tasirantu daga salafiyyawa da kasashen da ke daure musu gindi.
3349323