IQNA

Tafsirin Kur’ani Na Imam Ridha (AS) Ya Yi Daidai da Bukatar Zamanin Yau

23:53 - August 22, 2015
Lambar Labari: 3350066
Bangaren kasa da kasa, Hojj. Zakzaki a taron masu hidima na Imam Ridha (AS) ya bayyana cewa; tafsirin kur’ani mai tsarki na Imam Ridha (AS) ya yi daidai da dukkanin zamunna kamar yadda ya dace da zanin yau.


Kamfanin dillancin labaran Iqna daga wurin taron masu hidima na duniya na Imam Ridha (AS) ya habarta cewa, jagoran mabiya tafarkin shi’a a Najeriya sheikh Zakzaki fadi a gaban taron cewa, idan aka yi lakari za a ga cewa tafsirin kur’ani mai tsarki na Imam Ridha (AS) ya yi daidai da dukkanin zamunna kamar yadda ya dace da zanin yau da muke rayuwa, kuma  alokacin da ya rayu yana cikin bakunci ne, amma yanzu bakuncisa yak are.

A cikin bayanin nasa ya ce jam’a da dama ba su san Imam Ridha (AS) amma a cikin lokutan nan musammana  cikin azumin watan Ramadan mai alfarma, an gudanar da tafsirin kur’ani musamamn wanda ya kebanci Imam Ridha (AS) wanda bayanansa masu albarka kan tafsirin kur’ani ne aka yi ta mayar da hankali a kansu a tafsirin wannan shekara.

Wannan lamari ya zama abu mai jan hankali matuka ga mutane, domin kuwa ba su san wane ne shi Imam Ridha (AS) ba, amma albarkacin bayanan da suka ji hakan ya yi musu tasiri matuka, kuma daga yanzu sun samu wata matashiya dangane da wannan imami mai girman matsayi a wajen Allah madaukakin sarki.

Haka nan kuma yan kara da cewa daga wannan lokaci za a rika gudanar da taruka na musamman a lokutan tunawa da shi Imam Ridha (AS) da ma sauran ahlul bait (AS) domin tunawa da su da kuma bayanin matsayinsu a cikin addinin muslunci, domin mutane su kara samun haske kan tafarkin iyalan gidan manzo.

Sheikh Zakzaki ya kara da cewa a kimanin shekaru uku da suka gaba sun zo nan kasar kuma sun karbi tutar hubbaren Imam Ridha (AS) suka tafi da ita zuwa Najeriya, inda suka dora ta kan tulluwar husainiyarsu, tare da halartar dubban jama’a wajen taron.

An gudanar da wannan taro na masu hidima ga Imam Ridha (AS) ne tare da halartar malamai da kuma jami’ai da suka hada da Abu Zar Ibrahimi Turkamani shgaban cibiyar yada al’adun muslunci, Sayyid Jawad Ja’afari shugaban cibiyar kula da hubbaren Imam Ridha (AS) Muhammad Nahawandiyan shugaban ofishin shugaban kasa, Ayatollah Muteza Jabal Amuli daya daga cikin masu hidima ga hubbaren Imam Ridha (AS) da suka halarci wurin.

3349887

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha