Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Filadelfia tribune cewa, wannan baje koli yana daya daga cikin irinsa da aka gudanar a wannan jami’a.
Babbar manufar gudanar da wannan baje koli dai it ace fito da wasu daga cikin dadadn abubuwa masu kima da hakan ya hada da wannan kur’ani mai tsarki wanda asalinsa mallakin mutum dan kasar Iran ne da yake zaune a can kasar ta Amurka.
Yanzu haka dai akwai abubuwa 10 masu tsarki da aka nuna a wannan taron baje koli da ke gudana a babban dakin baje koli na wannan jami’a, wanda kuma jama’a sun bas hi muhimanci matuka fiye da yadda aka yi zato.
Daga cikin abubwan kuwa har da littafin Injila sabon alkawali na 12 na Sen Matio da aka rubuta a cikin shekara ta 1599 da a ka rubya akasar Jamus a wancan lokacin, bayanan kuma akwai littafin da aka sam wanda ke bayani kan ruwan tufan a lokacin annabi Nuh wanda yake da shekaru kimani 3500 a duniya.
Yayin da shi kuma wannankur’ani na Iran aka rubnta da rubutu wanda yake yake nuna dadden rubtu na kasar kamar yadda kuma aka samu an kawata shi da azurfa kamar dai yadda yake a’ada ce gare su suna rubuta littfai su yi musu kawa da haka, an rubuta shi a cikin shekara ta 1164.
Yayin da shi kuma littafin da ke bayani kan annabi Nuh (AS) da kuma ruwan tufana da ya afku alokacinsa aka samu wani bangare daga cikinsa da ke bayani har shafka biyu, a ranar 16 ga watan Aban za a gudanar da wani baje kolin sauran kayayyakin.
3349672