Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nan a Alalam cewa, mutanen palastinu sun gabatar da bukata ga majalisar dinkin duniya kan ta amince ta saka tutarsu a cikin tutoci na duniya masu kadada a gaban babban ginin ofishinta, tare da na fadar Vatican a cikin kasashe 193.
A cikin shekara ta 2012 Vatican ta zama mamba amajlaisar, wasu daga cikin wakilan wasu daga cikin kasashen larabawa da ke majalisar dinkin duniya suka gabatar da wannan bukata da nufin kara matsa lamba kan haramtacciyar kasar yahudawa da ta amince da batun kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Ana ganin idan dai har wannan lamari ya tabbata, kafin 15 ga Satumba to hakan zai kara nuna wa duniya cewa a halin yanzu haramtacciyar kasar yahudawa ta zama saniyar ware, ta yadda kasashen duniya a aikace sun nuna amincewa da samuwar kasar palastinu mai yanci.
Kamar yadda aka bayyana daga tutar dai ba shi nufin palastinu ta zama kasa mai cikakken iko kamar kowace kasa ta duniya, amma a siyasance hakan yana dauke da babban sako ga al’ummomin duniya, da ke tabbatar da an kama hanyar kafa kasar palastinu.
A daidai kudirin da aka gabatar ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, Palastinu da Vatican ne za a daga tutocinsu, a matsayin masu sanya ido a majalisar, ba a matsayin kasashe masu zaman kansu ba da ke majalisar.
Mahmud Abbas da Netanyahu za su halarci taron majalisar a ranar 25 ga watan Satumba a babban zauren majalisar, kuma Paparoma Francis na Catholic, inda zai sanar da amincewarsa da kasar Palastinu.
3353240