IQNA

Baje Kolin Kayayyakin Al’adun Muslunci A Birnin Lagos Nigeria

23:13 - September 01, 2015
Lambar Labari: 3357102
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a bude wani babban baje kolin kayayyakin da suka shafi al’adu da fasaha ta muslunci mai take takin Sulhu a birnin Lagos na tarayyar Nigeria.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na This Day Live cewa, wannan baje koli ana gudanar da shi ne karkashin kulawar cibiyar ilimi da kuma jin dadin musulmin Najeria ne wadda kuma cibiya ce da ke gudanar da ayyuka na jin kai a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya tana gudanar da ayyuka na taimaka mabiya addinin muslunci a fadin kasar, kamar yadda kuma tana gudanar da wasu ayyukan da suka danganci zaman lafiya da kuma sulhunta jama’a, haka nan kuma tana taimakon dalibai marassa galihu da ma sauran jama’a wadanda ba musulmi ba.

Daga abubuwan da za a gdanar a gefen wannan baje koli akwai tattaunawa tsakanin mabiya addinai domin kara samun fahimtar juna da zamantakewa mai kyaua  tsakaninsu.

A taron tattaunawar za a samu halartar wakilai na mabiya addinin muslucni da kuma mabiya addinin kirista na kasar, inda dukkanin bangarorinbiyu za s gababtar da bayanai domin kara kusanto da fahimtar juna a tsakaninsu.

Musulmin Nigeria dais u ne kasha 55 yayin da kuma kiristoci su ne kasha 40 n adukkanin yawan mutanen kasar.

3354626

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha