IQNA

‘Yan Ta’addan Kungiyar Daesh Sun Fi Muni A Kan ‘Yan Nazy

21:47 - September 03, 2015
Lambar Labari: 3357686
Bangaren kasa da kasa, Tony Abbott firayi ministan kasar Australia ya bayyana cewa yan ta’adda na kungiyar Daesh sun fi muni a kan ‘yan Nazy duk kuwa da barnar da suka yi a yakin duniya na biyu.


Kamfanin dillancin labaran iana ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na News24 cewa, Tony Abbott firayi ministan kasar Australia a zanatawarsa da tashar 2GB ta birnin Sydney, ya fadi  cewa yan ta’adda na kungiyar Daesh sun fi muni a kan ‘yan Nazy a yakin duniya na biyu duk kuwa da barnar da suka yi a lokacin.

Ya ci gaba da cewa a lokacin da aka yi yakin dniya an yan Nazy sun aikata muggan laifuka masu matukar muni, amma kma suna jin kunyar su nuna ma duniya, a kan haka suka rika boye abin da suka yi a lokacin, amma kuma yan ta’addan Daesh suna alfahari da ta’addancin da suke aikatawa.

Tony Abbott ya ce Daesh sun yi kama da mutanen Barbar da ake bayar da tarihinsu da cewa bas u da rahama da tausayin yan adam, wanda abin da suka aikata idan ana karantawa sai hankalin mutum ya tashi ya kidime.

Ya kara da cewa ya zama wajibi a kan dukkanin al’ummomin duniya da su mike kai da fata domin ganin an kawo karshen wannan kungiya ta ta’addanci ko ta wane hali, domin kuwa abin da suke yi ba zai bar kowa ba.

Furucin nasa dai ya fuskanci kakakusar suka daga kungiyoyin yahudawa na kasar Australia, sakamakon kwatanta Daesh da kuma yan Nazy .

3357605

Abubuwan Da Ya Shafa: australia
captcha