IQNA

Kungiyar ‘Yan ta’adda Ta Daesh Ta Dauki Alhakin Harin Birnin Sana’a

21:49 - September 03, 2015
Lambar Labari: 3357687
Bangaren kasa da kasa, kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta dauki alhakin ta’addancin da aka kai kan masallacin Mu’ayyid na birnin Sana’a a kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, kungiyar ‘yan ta’addan Daesh ta dauki alhakin ta’addancin da aka kai kan masallatan yankin Mu’ayyid  da kuma Jarraf da ke birnin Sana’a a kasar Yemen da ya yi sanadiyyar yin shahadar mutane 32 da kuma jikkatar wasu da dama.
A kwanakin baya kungiyar ta kaddamar da wasu hare-haren makamantan hakan a wani masallaci na mabiya tafarkin shi’a a yankin Qubad Mahdi a cikin birnin San’a, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 tare da jikkatar wasu 7 na daban.
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa cewa da Red cross ta sanar da dakatarda ayukan ta na wani dan lokaci a birnin aden na kasar Yemen bayan wani hari da wasu mayaka da ba’a san ko suwa ne ba suka kaiwa offishin na ta.

 

Kamar yadda Kakakin kungiyar ta red cross rima kamal ta sanar ga kanfanin dilancin labaren faransa ta ce wasu mutane ne daukeda makami suka farmawa offishin nasu inda suka kwashe masu kayan aiki da kuma kudade.

Hakan a cewar ta ya cilasta masu dakatarda aiki na dan wani lokaci a aden din birni na biyu mafi girma a kasar ta Yemen.

 

Hakazalika jami’ar ta kara da cewa tuni aka kwashe dukkan ma’aikatan kungiyar wadanda ‘yan asalin kasashen waje ne, inda aka nufi dasu wasu biranen kasar saboda kare lafiyar su.

3357593

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha