IQNA

Nutsewar Yaro Karami dan Syria A Gabar Ruwan Turkiya Kalu Bale Ne Ga ‘Yan Adamtaka

23:42 - September 05, 2015
Lambar Labari: 3358339
Bangaren kasa d akasa, Ahmad Tayyib babban malamin Azahar ya bayyana mutuwar karamin yaro dan Syria a ruwan Turkiya da cewa abin takaici ne ga lamirin ‘yan adamtaka.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Quds Al-arabi cewa, Shekhul Azhar ya bayyana cewa mutuwar karamin yaro dan Syria a ruwan Turkiya da cewa yana daga rai matuka kuma abin takaici ne.

A bangare guda kuma a yau asabar motocin farko dake dauke da bakin haure, sun tashi daga kasar hungary zuwa majar , bayan da mahukunta kasashen da suka amince su karbi dubun dubatar bakin dake yashe.

Lamarin bakin haure ya dauki hankulan duniya cikin wannan makon, bayanda wani kwale kwale ya kife a kan tekun kasar turki, inda mutane da dama suka rasa rayukan su, ciki kuwa har da wani yaro mai shekaru  dan kasar sham.

Y ace kafin wannan lokacin al’ummar wannan kasa suna zaune lami lafiya ba tare da wata matsala ba irin wannan, amma bayan haifar da rikici a kasar da tashe-tashen hankula, ga yadda lamarin koma a hakin yanzu.

Daga karshe ya kirayi kasashen da suke da fada a ji kan wannan lamari da su taka rawar da ta dace domin tabbatar da cewa an kawo karshen balai da ya addabi kasashhen musulmi da larabawa.

3358007

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha